Alhamis 13 Agusta 2026 - 22:27
An Gudanar da Zaman Juyayin Wafatin Manzon Allah (S) a Garuruwa Daban-daban na Najeriya da Jamhuriyar Nijar

Hauza/ Najeriya: A daidai lokacin da ake tunawa da ranar wafatin Manzon Allah (S), mabiya Ahlul-Baiti (AS), Musulman Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zaman juyayi a garuruwa daban-daban domin girmama tunawa da Manzon Allah (S) da koyarwarsa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a ranar 28 ga Safar 1448H, mabiya Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) sun gudanar da zaman juyayin wafatin Manzon Allah (S) a wurare daban-daban na Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da halartar dimbin masoya manzon Allah (S).

An gudanar da wadannan taruka a Kano, Potiskum, Illela, Lafia da Ƙwanni da sauran wurare, inda dimbin Musulmi, maza da mata, suka halarta.

A Kano, an gudanar da zaman juyayi a Hussainiyyar Imam Ridha (AS), inda aka fara taron da addu'a, sannan Sheikh Imamu Yakubu Kurna ya gabatar da jawabi kan matsayi da darajar Manzon Allah (S).

A Potiskum kuma, an gudanar da zaman juyayi a Makarantar Fudiyya ta Potiskum, inda Sheikh Ahmad Alhaji Ibrahim ya gabatar da jawabi. A karshen taron, Malam Ibrahim Lawan, wakilin ƴan’uwa na yankin Potiskum, ya yi takaitaccen jawabi tare da kira ga mahalarta da su shirya domin gudanar da bukukuwan Maulidin Manzon Allah (S) da ke gabatowa.

A Illela, da ke Jihar Sakkwato, an gudanar da zaman juyayi tare da addu'o'i da wakokin makoki. Malam Muhammad Bin Isma'il, wakilin mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a garin Illela, ya gabatar da jawabi.

Haka kuma, a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, mabiya Harkar Musulunci sun gudanar da zaman juyayin wafatin Manzon Allah (S). Malam Muhammad Nuruddeen Ahmad, wakilin ƴan’uwa na Da'irar Lafia, ya yi jawabi kan wafatin Manzon Allah (S), inda ya bayyana cewa Manzon Allah (S) ya kammala isar da sakon Allah kafin wafatinsa. Ya kuma jaddada muhimmancin Wilayar Amiril Muminina (AS) Imam Ali , tare da yin tsokaci kan wasu abubuwan da suka faru a kwanakin ƙarshe na rayuwar Manzon Allah (S).

A Ƙwanni ta Jamhuriyyar Nijar kuma, an gudanar da zaman juyayi a Masallacin Marigayi Alhaji Buro da ke Tsohuwar Tashar garin. Malam Sani Isma'il Ƙwanni ne ya gabatar da jawabi a wajen taron.

Gudanar da wadannan taruka a wurare daban-daban ya kasance wata alama ce ta nuna ƙauna da girmamawa da Musulman Najeriya da Jamhuriyyar Nijar, musamman mabiya Ahlul-Baiti (AS), suke yi wa Manzon Allah (S), da kuma jajircewarsu wajen raya tunawa da rayuwarsa, tarihinsa da koyarwarsa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha